Ina sayen ƙafafu biyu na mutum kan naira dubu 20 – matsafi

1683226078375
1683226078375

Wani tshon matsafi mai suna Ifasoji Ayangbesan, wanda aka kama da zargin kisa da kuma yin gunduwa-gunduwa da gawar wata matashiya mai suna Oyindamola Adeyemi, ya ce ya sayi ƙafafu biyu na mutum kan 20,000.

A makon da ya gabata ne, rundunar ƴan sanda a jihar Ogun, ta fitar da wata sanarwar kama Ayangbesan, inda ta zarge shi da bai wa ƴan sanda cin hancin miiyan ɗaya domin su sake shi.

Yayin da aka gabatar da shi gaban manema labarai, ya musanta kashe matashiyar wadda aka ruwaito kisan ta a ranar 28 ga watan Janairun 2023.

Ya yi iƙirarin cewa shi mai sayar da maganin gargajiya ne ba masafi ba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here