Wata babbar kotun tarayya da ke zaman ta a Abuja ta soke tare da jingine zabukan fidda gwani na gundumomi da na kananan hukumomi da jam’iyyar APC ta gudanar a ranar 7 ga watan Fabrairu a Kogi domin tsaida ‘yan takararta a zaben gwamna da za a yi a watan Nuwamba.
Wasu fusatattun ayarin ‘ya’yan jam’iyyar APC a karkashin jagorancin Realwan Okpanachi sun garzaya kotu domin neman soke gangamin guda biyu da aka gudanar a jam’iyyar a jihar.
Mai shari’a James Omotosho yayin da yake yanke hukunci a ranar Laraba ya haramtawa hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), yin amfani da jerin sunayen wakilan da ba bisa ka’ida da jam’iyyar ta fitar na zaben dan takarar gwamna.
Kotun ta soke zanukan biyu ne saboda ba a gudanar da su kamar yadda dokar zabe ta 2022 da kuma kundin tsarin mulkin jam’iyyar APC suka yi ba.
Muna tafe karin bayani gaba kadan…










































