Zuwa yanzu ‘yan bindiga sun saki ɗalibai 120 na makarantar Bethel Baptist Kaduna – CAN

THE REALSED BETHEL BAPTIST HIGH SCHOOL STUDENTS IN KADUNA. 4 1024x683 2
THE REALSED BETHEL BAPTIST HIGH SCHOOL STUDENTS IN KADUNA. 4 1024x683 2

Shugaban kungiyar Kiristocin Najeriya CAN reshen jihar Kaduna, Rabaran John Hayab, ya tabbatar da cewa kawo yanzu an kubutar da dalibai 120 da aka sace na makarantar sakandaren Bethel Baptist da ke jihar Kaduna.

A wata sanarwa da ya fitar a Kaduna ranar Asabar, Hayab ya tunatar da cewa da sanyin safiyar ranar 5 ga watan Yuli, 2021, ‘yan bindiga sun kai farmaki makarantar da ke Maraban Damishi a karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna inda suka yi garkuwa da dalibai 121.

Ya ce adadin daliban da aka saki sun hada da dalibi daya da aka sako a ranar 28 ga watan Disamba, 2021 da kuma wani wanda aka sake a ranar 1 ga watan Janairu.

“Da sakin wadannan dalibai guda biyu, adadin dalibai 120 ne suka samu ‘yancinsu ya zuwa yanzu kuma dalibi daya ne ke hannun ‘yan fashin,” in ji shi.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here