Kwalejin fasaha ta jihar Kano, ta sha alwashin bada dukkan goyon baya, domin sauya tunanin matasa daga shaye-shaye da daba zuwa neman ilimi da kuma dogaro da kai.
Shugaban kwalejin Dakta Abubakar Umar Faruk, ne ya bayyana hakan a zantawarsa da manema labarai, ranar Asabar a ofishinsa.
Karanta wannan: Kwalejin fasaha ta jihar Kano za ta fara kwasa-kwasai ta kafar Internet
Yace, kwalejin ta himmatu wajen horas da matasa, maza da mata sana’ion da za su dogara da kansu, tare kuma da samun takardar shaidar karamar Diploma (National Diploma) da kuma babbar Diploma (Higher National Diploma).
Ya kuma ce ta hakan ne za’a sauya tunanin matasan dake shaye-shaye ko fadan daba, zuwa turbar ilimi da kuma dogaro da kansu, a lokutan da basa zuwa makaranta.
Karanta wannan: Gwamnatin Kogi ta haramta bada lasisi ga masu hako Ma’adanai a Jihar
Ya kara da cewa, matukar al’umma ta rungumi Ilimi da sana’oin dogaro da kai, toh babu shakka za’a rage yawan aikata laifuka a cikin jihar Kano da ma kasa baki-daya.
Ya bukaci manyan ‘yan kasuwa da kanana da ke jihar Kano da sauran jahohi, su fito da sabbin tsare-tsare, ta yadda za su ci gajiyar duk tallafin da gwamnati ko kungiyoyin agaji ke bayarwa.













































