Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ce za ta ci gaba da biyan tallafin Naira 35,000 da ta fara biyan ma’aikata domin rage radadin illar cire tallafin man fetur ga ma’aikatan ƙasar.
Gwamnatin ta kuma roki kungiyar kwadagon kasar NLC da su janye yajin aikin da suka shirya yi na kwanaki 14.
Karamar ministar Kwadago ta kasa, Nkeiruka Onyejeocha ce ta bada wannan tabbacin a Abuja a wajen wani taro da shugabannin ƙungiyoyin kwadagon biyu da aka yi kan wa’adin da suka bai wa gwamnati na tafiya yajin aiki idan ba ta cika musu bukatunsu ba a cikin makonni biyu.
Karanta wannan: Fashewar iskar Gas ya rusa shaguna 18 a Legas
An dai cimma yarjejeniyar ne ranar 2 ga watan Oktobar 2023 mai dauke da abubuwa 16 da suka hada da ƙarancin albashin ma’aikata da tallafin Naira 35,000 ga ma’aikata duk wata da dai sauransu.
Onyejeocha ta kuma ce gwamnati ta kara kaimi wajen ganin an kammala aiwatar da wannan yarjejeniya.
Ministar ta kira taron ne domin bayyana wa ƙungiyoyin kwadagon yadda ake aiwatar da yarjejeniyar, da kuma jaddada aniyar gwamnati kan yarjejeniyar.
Karanta wannan: Dakataccen shugaban jam’iyyar PDP na Jihar Ondo ya rasu
“Gaskiya ne duk da cewa mun kulla yarjejeniya, amma gwamnati ta nuna gaskiya kan wannan batu, kuma bisa la’akari da gaggawar lamarin ne na kira wannan taro domin tattaunawa ita ce hanya mafi dacewa akoda yaushe, kuma dukkan mu muna neman lafiya kasancewar mutanenmu.” inji ta.
Ta yi nuni da cewa, yayin da martanin kungiyoyin kwadagon kan gazawar gwamnati na cika yarjejeniyar bai dace ba, yana da kyau ayi la’akari da cewa wasu abubuwa da ke cikin yarjejeniyar ba za’a iya cimma musu ba a lokaci guda.
Rahotanni sun ce an tashi daga taron ba tare da cimma wata matsaya dangane da bukatun ba.