Wani mummunan hatsari ya afku a ranar Laraba yayin da wata babbar mota ta murkushe mutane biyu har lahira a Kano, daura da titin filin jirgin sama.
Mai magana da yawun hukumar kiyaye haddura ta kasa (FRSC) reshen jihar Kano CRC Abdullahi Labaran, ya ce hatsarin ya faru ne sakamakon tukin ganganci wanda ya hada da wata motar DAF da babur Jincheng.
A wata sanarwa da ya fitar ya ce hatsarin da ya afku da misalin karfe 8.15 na safe ya rutsa da mutane shida, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane biyu da kuma wadanda suka samu mummunan rauni.
Karanta:Sallah: Dalilan da suka sa sarkin Kano na 15 Aminu Ado ya soke hawan sallah
Ya ce a lokacin da aka samu wannan kiran na gaggawa, jami’an hukumar sun je wajen tare da kwashe gawarwaki daga inda hatsarin ya afku yayin da aka kai wadanda suka jikkata zuwa asibiti domin kula da lafiyarsu.
Sai dai wani ganau, Dennis Peter ya ce lamarin ya kai ga mutuwar mutane uku.
Peter ya ce hatsarin ya faru ne lokacin da babbar motar ta kutsa cikin babur din da ke dauke da mutanen da suka mutu lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane uku a nan take.













































