Wasannin Afirka: Falconets za ta fafata da Ghana a wasan karshe

Falconet, wasannin, afrika, ghana, karshe
Tawagar kwallon kafar mata ta Najeriya ta 'yan kasa da shekaru 20 Falconets, za ta kara da Ghana ranar Alhamis a wasan karshe na wasan kwallon kafa na mata a...

Tawagar kwallon kafar mata ta Najeriya ta ‘yan kasa da shekaru 20 Falconets, za ta kara da Ghana ranar Alhamis a wasan karshe na wasan kwallon kafa na mata a gasar cin kofin Afrika karo na 13 a Ghana.

NAN ta rawaito cewa Falconets sun samu damar zuwa wasan karshe, bayan da suka doke Uganda da ci 2-0 a wasan da suka buga a filin wasa na Cape Coast ranar Litinin a wasan kusa da na karshe.

Ghana ta kuma doke Teranga Lionesses na Senegal da ci 3-1 inda suka samu tikitin zuwa wasan karshe.

Karin labari: Da Dumi-Dumi: Mutane 2 sun jikkata a harin Bam a jihar Borno

Za’a yi wasan karshe ne tsakanin Najeriya da mai masaukin baki Ghana a filin wasa na Cape Coast ranar Alhamis da karfe 8 na dare.

A halin da ake ciki, Uganda za ta kara da Senegal domin fafatawa da samun lambar tagulla a gasar da za’a yi a filin wasa na Cape Coast a ranar Alhamis da karfe 5 na yamma.

Karin labari: Sojojin Habasha sun kashe mayakan sa kai 150 a Amhara

A shekarun baya Falconets dai ta lashe lambar zinare a gasar Afrika karo na 12 da aka yi a Rabat na Morocco, a shekarar 2019.

Za’a kawo karshen wasannin Afirka karo na 13 a ranar 8 ga watan Maris da ranar 23 ga watan Maris.

Ana ci gaba da gudanar da wasannin a birane uku na Accra da Kumasi da kuma Cape Coast.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here