Janar Godwin Osagie Abbe, tsohon ministan tsaro da harkokin cikin gida ya rasu.
Abbe, wanda kuma tsohon gwamnan jihar Akwa Ibom ne a lokacin mulkin soja a tsakanin 31 ga Yuli, 1988, da 5 ga Satumba, 1990, da kuma jihar Ribas tsakanin watan Agusta 1990 zuwa Janairu 1992, ya rasu ne a Abuja ranar Asabar bayan ya sha fama da rashin lafiya.
Sanatan jihar Edo, Monday Okpebolo, ya yi alhinin rasuwar marigayi Janar, wanda ya bayyana a matsayin babban dan jihar.