Ƙungiyar Jami’an ƴan sandan Najeriya da suka yi ritaya ta sha alwashin yin zanga-zangar lumana boyo bayan buƙatarta ta neman a cire jami’an ‘yan sanda da ke bakin aiki daga tsarin fansho, wanda a cewarsu ya jefa su cikin mawuyacin hali musamman ma a fannin tattalin arziki da talauci da kuma tashin hankali da bakin ciki har ma da rasa ran wasu daga cikin abokansu da suka yi ritaya.
Kungiyar ta jaddada cewa za a gudanar da zanga-zangar ne cikin lumana da kuma zagayawa a dukkan jihohin Najeiya 36.
Sanarwar da kungiyar ta fitar ta kara da cewa, “A matsayinmu na ‘yan kasa masu bin doka da oda, za mu ci gaba da jaddada bukatarmu ta neman a cire ‘yan sandan Najeriya daga tsarin fansho ta hanyar lumana har sai an ji muryoyinmu.”
Kungiyar ta yi tsinkayen wata zanga-zanga da ta yi daga ranar 24 ga watan Fabrairu zuwa 3 ga Maris, na bana a zauren Majalisar Dokoki na jihohin Kaduna da Bauchi, inda aka gabatar da koke ga wasu muhimman ofisoshi guda biyar da suka hada da shugabannin kwamitocin Majalisar Dattawa da na Majalisar tarayya da abun ya shafa da kuma Daraktan Ma’aikatar Ayyuka ta Jiha.
Sai dai wadanda suka yi ritayar sun nuna rashin jin dadinsu game da shirun da Majalisar ta yi, musamman dangane da sakamakon jin ra’ayin jama’a kan dokar Hukumar Fansho ta ‘yan sanda da aka gudanar a ranar 19 ga Nuwamba bara.
Sun kuma nesanta kansu daga duk wata kungiya da ke shirya zanga-zangar tarzoma.
Haka kuma, ƙungiyar ta dage cewa kafa hukumar fansho ta ‘yan sanda mai zaman kanta ita ce hanya daya tilo da za ta iya magance abin da suka bayyana a matsayin rashin adalci a tsarin fansho na yanzu.













































