Shugaban Najeriya Bola Tinubu zai tafi ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa domin halartar taron ɗorewar tattalin arziki na duniya ta 2025 (ADSW 2025).
Shugaban ƙasar, Sheikh Mohamed bin Zayed Al Nahyan ne ya gayyaci shugaba Tinubu domin halartar taron – wanda zai gudana tsakanin 12 zuwa 18 ga watan Janairu.
Taron – wanda zai samu halartar manyan shugabannin duniya, da masana da ƙungiyoyin fararen hula da ‘yan kasuwa da masu ruwa da tsaki – zai tattauna nasarorin da aka samu a fannin tattalin arziki da zamantakewa, tare da lalubo hanyoyin ɗorewar ci gaban da aka samu.
Cikin sanarwar bulaguron da fadar shugaban Najeriya ta fitar, ta ce a taron Shugaba Tinubu zai jaddada manufofin gwamnatinsa, ciki har ci gaban tattalin arziki da makamashi da sufuri da fannin lafiya.
Haka kuma tawagar Najeriya a taron za ta gana da fadar sarkin ƙasar domin tattauna batutuwan da suka shafi ƙasashen biyu.
Ministan harkokin wajen ƙasar, Ambassador Yusuf Tuggar na daga cikin manyan jami’an gwamnatin da za su yi wa shugaban rakiya a taron, a cewar sanarwar.
Ana sa ran shugaban zai koma Najeriya bayan kammala taron ranar 16 ga watan Janairu.