Kakakin majalisar wakilan Najeriya Femi Gbajabiamila yayi sabon nadi a ofishin sa damun gudanar da aikin sa yacce ya kamata.
Nadin dai ya biyo bayan ajiye aiki da wasu daga cikin ma’aikatan majalisar dokokin sukai domin shiga zaben shekarar 2023, kamar yacce doka ta tanadar duk wanda yake neman tsayawa takara sai ya ajiye aikin sa.
Wadan da aka nada sun hada da Olanrewaju Smart Wasiu, a matsayan shugaban ma’aikata, da kuma Olufunmi Badmus a matsayin mataimakin shugaban ma’aikata.
Sauran wadan da aka nada sun hada da Abdulrauf Modibbo, Lamir Umar Ibrahim, Chief Kenneth Uzoigwe, Barr Bisi Irinoye, Ibrahim Ladega, Jamila Muazu, Barr Obiageli Onu, Kunle Bello.
Kakakin ya shawarci wadan da ya bawa mukamai da su bi dokokin aiki da kuma rukun gaskiya da amana.
(Lanre Lasisi)












































