Shekara 65 da samun ƴancin kai: Gwamnatin tarayya ta ayyana 1 ga Oktoba a matsayin ranar hutu

Minister of Interior Dr. Olubunmi Tunji Ojo (1)

Gwamnatin tarayya ta ayyana ranar Laraba, 1 ga watan Oktoba, a matsayin ranar hutu domin bikin cikar Najeriya shekaru 65 da samun ‘yancin kai daga Turawan mulkin mallaka.

Ministan harkokin cikin gida, Dakta Olubunmi Tunji-Ojo ne ya bayyana hakan a ranar Litinin ta cikin wata sanarwa da babbar sakatariyar ma’aikatar, Dakta Magdalene Ajani, ta sanya wa hannu.

Karanta: Babbar jojin Najeriya ta rantsar da sababbin lauyoyi 57 da suka samu matsayin SAN

A cikin sanarwar, ministan ya taya ‘yan Najeriya murnar wannan babban tarihi, yana mai jaddada muhimmancin kishin ƙasa, haɗin kai da juriya da suka kasance ginshiƙan da suka tabbatar da dorewar ƙasar tun daga shekarar 1960.

Tunji-Ojo ya kuma yi kira ga ‘yan Najeriya da su ci gaba da ba da goyon baya ga tsarin sabon fata na Shugaba Bola Ahmed Tinubu, wanda ya ce ya ta’allaka ne kan farfado da ƙasa, bunƙasa tattalin arziki da samar da walwala ga kowa da kowa.

Ya bayyana tabbacin cewa, idan aka yi aiki tare da haɗin kai, Najeriya za ta ci gaba da samun ci gaba cikin zaman lafiya, cigaba da bunƙasar tattalin arziki.

A ƙarshe, ministan ya yi fatan al’umma za su yi biki mai cike da annashuwa da tunawa mai tarihi a ranar tunawa da samun ‘yancin kai ta shekarar 2025.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here