Hukumar kula da yanayin ta ƙasa NiMet ta yi hasashen cewa za a samu yanayin ƙura daga ranar Asabar zuwa Litinin a fadin kasar nan.
A hasashen yanayin da hukumar ta fitar a Abuja, ta ce za a samu matsakaicin kura tare da iya hangen nesa tsakanin kilomita biyu zuwa biyar a yankin arewacin kasar a ranar Asabar.
Ta kuma bayyana cewa ana iya samun karancin hangen nesa da bai wuce mita 1,000 ba a wasu sassan jihohin Katsina da Kano da Jigawa a duk tsawon lokacin hasashen.
Hukumar ta kuma yi hasashen matsakaicin ƙura a yankin Arewa ta Tsakiya a tsawon lokacin da aka ambata.
Haka kuma ta yi hasashen sararin samaniya mai rana tare da ɗan gajimare a yankin kudancin kasar, tare da yiwuwar samun tsawa da ruwan sama kadan da rana ko yamma a wasu sassan jihohin Lagos da Bayelsa da Delta da Rivers da Cross River da Akwa Ibom.
NiMet ta kuma yi hasashen matsakaicin ƙura a yankunan Arewa da Arewa ta Tsakiya a ranar Lahadi a tsawon lokacin hasashen.
Ta kara da cewa za a samu sararin samaniya mai rana tare da ɗan gajimare a kudancin kasar, tare da yiwuwar samun tsawa a wasu wurare da ruwan sama kadan a jihohin Ondo da Bayelsa da Rivers da Delta da Edo a karshen rana.
A cewar NiMet, za a samu karamar ƙura a yankin Arewa a ranar Litinin yayin da ƙurar za ta ci gaba a yankin Arewa ta Tsakiya a tsawon lokacin hasashen.
Ta kuma bayyana cewa za a samu sararin samaniya mai rana tare da ɗan gajimare a kudancin kasar, tare da yiwuwar samun tsawa a wurare daban-daban da kuma ruwan sama kadan a jihohin Lagos da Edo da Delta da Bayelsa a karshen rana.
Hukumar ta ce ƙura za ta ci gaba da kasancewa a sararin samaniya, don haka ta bukaci jama’a su dauki matakan kariya da suka dace, musamman masu fama da cutar asma da sauran matsalolin numfashi.
Ta kuma shawarci direbobi da su yi taka-tsantsan yayin da ake ruwan sama, yayin da kamfanonin jiragen sama su rika samun rahotannin yanayin sararin samaniya na filayen jiragen sama daga NiMet domin inganta shirye-shiryen aikinsu.
Haka kuma ta bukaci mazauna kasar da su rika bibiyar sabbin bayanan yanayi ta hanyar ziyartar shafin internet na hukumar.











































