Hukumar NDLEA ta kama miyagun kwayoyi da suka hada da methamphetamine da Loud, wani nau’in wiwi mai karfi, wadanda aka boye a kayayyakin gyaran mota da aka shigo da su daga Canada.
Kudin kwayoyin da aka kama a tashar Tincan, Lagos, sun kai N3.3 biliyan, inda aka kama wasu mutum uku da ake zargi da hannu a safarar su.
A Port Harcourt kuma, hukumar ta kama kwalaben maganin tari na codeine har 636,600 daga India, wanda kudinsu ya kai N4.4 biliyan.
NDLEA ta bayyana cewa an bibiyi kayayyakin daga kasashen da aka fito da su har zuwa Najeriya, kuma tana ci gaba da yakin fadakarwa kan illar miyagun kwayoyi a makarantu da al’ummomi daban-daban a fadin kasar.













































