Gwamnatin tarayya ta sake nuna fushinta kan matakin da kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) ta dauka na shiga yajin aikin gargadi na mako 4, inda ta bayyana cewa sun dauki matakin ne yayin da ake tsakiyar tattaunawa.
Ministan Ilimi, Malam Adamu Adamu wanda ya bayyana hakan ga manema labarai a fadar gwamnatin jihar a karshen taron majalisar zartarwa ta tarayya, ya musanta cewa ya yi watsi da ganawa da kungiyar.
Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ne ya jagoranci taron a zauren majalisar da ke fadar shugaban kasa ta Villa, Abuja a ranar Laraba.
Kungiyar ASUU dai ta shelanta yajin aikin gargadi na wata daya a ranar Litinin din da ta gabata, saboda rashin warware wasu bukatu da suka ce gwamnatin tarayya ta ki biya.
Sai dai Ministan ya bayyana cewa shi ne ya kira taro da kungiyar ASUU a kokarin da ake na warware matsalolin da ake fuskanta.
Ya ce, “Abin takaici ASUU sun shiga yajin aikin, yayin da nake neman su domin magance matsalar.
“Abu na karshe da ya faru shi ne kwamitinmu ya duba bukatunsu amma ana cigaba da tattaunawa. Sun gabatar da daftarin yarjejeniya wanda ma’aikatar ke dubawa.”
Akan daftarin yarjejeniyar da ASUU, ya ce: “Kwamiti na duba lamarin. Idan an gama, daga nan gwamnati za ta sanar da abin da ta karba da wanda ta watsar, amma kwatsam na ji sun tafi yajin aiki.”













































