Babban mai kula da cibiyar yaki da ta’addanci ta ƙasa da ke ƙarƙashin ofishin mai ba shugaban ƙasa shawara kan tsaro, Manjo Janar Adamu Laka, ya nuna damuwa kan cewa wasu masu gudanar da harkar POS suna taka rawa wajen taimaka wa ayyukan ta’addanci da garkuwa da mutane a Nijeriya.
Ya bayyana hakan ne a wani taron bitar ƙarshen shekara da aka gudanar a birnin tarayya Abuja, inda ya nuna cewa a lokuta da dama kuɗaɗen fansa ana tura su ne zuwa asusun wasu masu POS, daga nan kuma a fitar da tsabar kuɗi a miƙa wa masu garkuwa, abin da ke sa bin sawun kuɗin ke zama da wahala.
Ya ƙara da cewa binciken da jami’an tsaro ke yi kan wasu canja wurin kuɗaɗe yakan nuna cewa asusun da aka tura kuɗin na masu POS ne, inda masu garkuwa ke bayar da lambar cibiyar, a tura kuɗin, sannan su je su karɓa.
Babban jami’in yaƙi da ta’addanci ya ce hukumomin tsaro sun ƙara kaimi wajen bibiyar kuɗaɗen fansa da kama waɗanda ke da hannu, da rushe hanyoyin tallafa wa ta’addanci ta fuskar kuɗi, duk da cewa ba za a iya bayyana cikakkun bayanai ba saboda dalilan tsaro.
Karanta: Kotu ta bayar da beli ga Malami, ta sanya ranar sauraron ƙara
Ya bayyana cewa an kama da gurfanar da mutane da dama dangane da biyan kuɗaɗen fansa da tallafa wa ta’addanci, tare da kwato kadarori da kwace wasu dukiyoyi, a matsayin wani ɓangare na bin ƙa’idojin ƙasa da ƙasa na yaƙi da wanke kuɗi da hana tallafa wa ta’addanci.
Laka ya ce ci gaban da Nijeriya ta samu kwanan nan wajen cika sharuɗɗan ƙungiyar aikin kuɗi ta duniya ya samo asali ne daga haɗin gwiwar bincike da wani kwamitin haɗaka ya yi, wanda ya haɗa da hukumomin tsaro, sassan tattara bayanan kuɗi da bangaren shari’a.
Ya amince da ƙalubalen sauyin dabarun ’yan ta’adda da kuma iyakokin yankin Sahel masu rauni, amma ya tabbatar wa ’yan Nijeriya cewa hukumomin tsaro za su ci gaba da ƙarfafa matakan yaƙi da ta’addanci ta fuskar zahiri da na fasahar zamani, tare da haɗin gwiwa da manyan dandalin sada zumunta domin gano da rufe asusun da ake amfani da su wajen tallata ayyukan laifi da tara kuɗi.













































