Majalisar zartarwa ta Jihar Kano ta amince da kashe Naira Biliyan 8.5 domin aiwatar da ayyuka daban-daban na more rayuwa, bangaren lafiya da ilimi a fadin jihar.
Ma’aikatar yada labarai da harkokin cikin gida ta jihar ta bayyana sakamakon taron majalisar karo na 37 da aka gudanar a gidan Malam Aminu Kano, masaukin gwamna da ke Abuja, inda aka tattauna muhimman batutuwan mulki da ci gaban jihar.
Daga cikin amincewar da aka bayar, an ware Naira miliyan 251.9 a matsayin diyya ga kadarorin da aikin gina titin mai tsawon kilomita biyar mai bangarori biyu ya shafa a karamar hukumar Bagwai, yayin da aka ware Naira 148.8 domin gina gidan marayu a gidan kula da yara na Nassarawa.
Majalisar ta kuma amince da Naira Miliyan 147.2 domin share fili da gina hanyar shiga kauyen Farin Ruwa–Yan Kwadi a karamar hukumar Shanono, sannan aka ware Naira 187.8 domin gina karin ginin ofisoshi da tsawaita katangar Hukumar Kula da Lafiya a matakin Farko ta Jihar.
Haka kuma an amince da Naira Miliyan 660.3 domin gina magudanan ruwa na kankare da shimfida tayil a yankin Ayagi-Aisami da ke mazabar Bakin Ruwa a karamar hukumar Dala, tare da Naira Biliyan 1.7 domin gina titin Chiromawa zuwa Garun Babba a karamar hukumar Garun Malam.
Majalisar ta amince da Naira Miliyan 677.6 domin sake ginawa da gyara da sabunta Asibitin Janar na Rogo da gobara ta shafa, da kuma Naira Miliyan 113.8 domin gyaran makarantar sakandaren ƙananan yara ta gwamnati da ke Tatsawarki a karamar hukumar Kumbotso.
Sauran amincewar sun hada da Naira Miliyan 830.2 a matsayin diyya ga gonakin da gina kananan madatsun ruwa guda biyar ya shafa a kananan hukumomi biyar, sai Naira Miliyan 176.2 domin gina Arewa Knot da rijiyar ruwa mai matakai a zagayen Alfurqan da Baban Gwari.
Hakazalika Naira Biliyan 3.1 domin samar da sinadarin aluminium sulphate ga wuraren ruwan sha na jihar na tsawon watanni shida, da kuma Naira Miliyan 520 domin sayen na’urar CT Scan ga Asibitin Koyarwa na Muhammad Abdullahi Wase.
A bangaren manufofi, majalisar ta yi Allah-wadai da mutuwar wata mara lafiya a asibitin kula da masu lalurar fitsari na Abubakar Imam tare da bayar da tabbacin kammala bincike da daukar matakan da suka dace.
Sannan majalisar ta amince da fara bunkasa yankin masana’antu na Ajaokuta–Kaduna–Kano a Tamburawa da kuma inganta cibiyar horaswa ta NYSC a Karaye.
NAN













































