Majalisar Dattawa: Ƙudirin dokar tilasta ilimin firamare a Najeriya ya tsallake karatu na 2

Majalisar, Dattawa, Ƙudirin, dokar, tilasta, ilimin, firamare, tsallake, karatu
Wani ƙudirin doka da ke neman samar da ilimi kyauta tare da tilasta sa yara makaranta a Najeriya ya tsallake karatu na biyu a majalisar dattawa. kamar yanda...

Daga: Sunusi A. Dantalata Fagge

Wani ƙudirin doka da ke neman samar da ilimi kyauta tare da tilasta sa yara makaranta a Najeriya ya tsallake karatu na biyu a majalisar dattawa.

kamar yanda sashin kundin tsarin mulkin kasar na UBE Act, 2004 ya tanadar.

An zartar da ƙudurin ne wanda Idiat Adebule, ƴar jam’iyyar APC daga Legas ta gabatar, bayan da yawancin sanatocin suka kaɗa ƙuri’ar amincewa da shi.

Ta kuma gabatar da hukuncin biyan Naira 250,000 ga iyayen da suka ƙi kai ‘ya’yansu makarantar firamare da sakandare.

Karin labari: Ministan kudi ya mikawa shugaba Tinubu mafi karancin albashin ma’aikata

Sashe na 2 na dokar UBE ya bayyana cewa kowace gwamnati a Najeriya za ta samar da ilimi kyauta, kuma wajibi ne ga kowane yaro da ya kai matakin firamare da ƙaramar sakandare.

Yayin da take jagorantar muhawara kan kudirin Misis Adebule, ta ce idan har aka amince da kudurin, zai rage yawan yaran da ba sa zuwa makaranta a Najeriya.

Ta ce galibin iyayen da ‘ya’yansu ba sa zuwa makaranta ba su damu ba saboda ba a hukunta su.

Karin labari: Tinubu zai kashe Tiriliyan biyar kan tallafin man fetur

Sanatar ta ƙara da cewa bai kamata talauci ya zama hujjar rashin samun ilimin kasashen yamma ba.

Misis Adebule, bayan haka ta yi kira ga ‘yan majalisar da su goyi bayan amincewa da kudirin.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here