Jagoran tafiyar Kwankwasiyya na ƙasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana cewa bai goyi baya ba kuma bai amince da shirin gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, da wasu ’yan NNPP na komawa jam’iyyar APC ba.
Wannan ya biyo bayan jawo hankalin al’umma kan wani rahoto mai ruɗani da wata jaridar Premium Times ta wallafa, wanda ya yi iƙirarin cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya amince ko ya goyi bayan shirin gwamnan Jihar Kano na komawa APC, lamarin da aka bayyana a matsayin ƙarya.
Wannan bayani ya fito ne cikin wata sanarwa da Saifullahi Hassan, hadimin yaɗa labarai na Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya fitar, inda ya bayyana cewa rahoton ba shi da tushe balle makama kuma ya kauce wa gaskiya.
Sanarwar ta nuna cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, a matsayinsa na jagoran jam’iyyar NNPP na ƙasa, yana nan daram kan manufofi, hangen nesa da ƙa’idojin jam’iyyar.
A cewar sanarwar, Abba Kabir Yusuf ya samu nasarar zama gwamnan Jihar Kano ne a ƙarƙashin tutar NNPP kuma har yanzu mamba ne na jam’iyyar.
Ta ƙara da cewa babu wani lokaci da Sanata Kwankwaso ya amince, ko ya goyi baya ko ya nuna yarda da duk wani shiri na gwamnan Kano na komawa APC, don haka duk wani rahoto da ke nuna akasin haka a matsayin gurɓata gaskiya da ya kamata a yi watsi da shi.
Sanarwar ta kuma buƙaci ’yan jam’iyya, magoya baya da kafafen yaɗa labarai da su yi watsi da bayanan ƙarya tare da dogaro da sahihan majiyoyi masu inganci domin samun sahihin bayani.
A ƙarshe, jaridar Solacebase “mun masu bayyana baƙin cikin mu kan kuskuren da aka samu a baya wajen fassara wani gidan bidiyo a harshen Hausa, da ke cewa Kwankwaso ya goyi bayan Abba ya koma APC da wasu yan jam’iyyar, a don haka muke neman afuwar jama’a bisa kuskuren fahimta da ya jawo wallafa rahoton da bai dace ba”.













































