Kwamishinan Kano ya fice daga NNPP

nnpp logo new 1

Kwamishinan Muhalli da Sauyin Yanayi na Jihar Kano, Dakta Dahiru Hashim, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar NNPP, inda ya ce murabus ɗinsa zai fara aiki nan take.

Rahotanni sun nuna cewa Dakta Dahiru Hashim, ya bayyana matakin ne ta cikin wata wasiƙar murabus da ya rubuta a ranar Juma’a, 23 ga Janairu, 2026, wadda ya aike wa shugaban NNPP na mazabar Gobirawa da ke ƙaramar hukumar Dala a Jihar Kano.

A cewarsa, ya ɗauki wannan mataki ne bisa kyakkyawar niyya da kuma la’akari da muradin al’ummar Jihar Kano gaba ɗaya, ba tare da wata ƙiyayya ko matsin lamba ba.

Kwamishinan ya bayyana cewa ficewarsa ta zo ne bayan dogon tunani, kuma ta yi daidai da shugabanci da tsare-tsaren Gwamna Abba Kabir Yusuf, wanda a ƙarƙashin mulkinsa ya ke ci gaba da hidimta wa al’umma a halin yanzu.

Haka kuma, Dakta Dahiru Muhammad Hashim, ya nuna godiya ga jam’iyyar NNPP bisa damar da ta ba shi, tare da yaba wa shugabanni da mambobin jam’iyyar, musamman a mazabar Gobirawa, bisa goyon baya, haɗin kai da mutunta juna da ya samu a tsawon lokacin da yake tare da jam’iyyar.

Ficewar Kwamishinan na zuwa ne awanni kaɗan bayan da Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, shi ma ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar NNPP, lamarin da ke nuna babbar sauyi a yanayin siyasar jihar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here