Babbar kotun jihar Kano ta bayar da umarnin dakatar da babban bankin kasa CBN ci gaba da rike kudaden asusun tarayya na kananan hukumomi 44 na jihar.
Wadanda suka shigar da ƙara sun hada da Shugaban NULGE, Ibrahim Muhd, Ibrahim Uba Shehu, Ibrahim Shehu Abubakar, Usman Isa, Sarki Alhaji Kurawa da Malam Usman Imam.
Masu shigar da kara, ta bakin lauyansu Bashir Yusuf Muhammad, sun shigar da kara mai kwanan ranar 1 ga watan Nuwamba, inda suka bukaci kotu ta hana wadanda ake karan hanawa ko jinkirta wasu kaso mafi muhimmanci ga kananan hukumomi a jihar.
Karin labari: NAHCON ta nemi CBN ta cire kashi 2% na kudaden Alhazai
Wadanda ake kara sun hada da: Akanta-Janar na tarayya (AGF), da CBN da hukumar kula da harkokin haraji (RMAFC) da kananan hukumomin Kano 44 da bankunan UBA, Access da wasu bankunan kasuwanci guda shida.
Da yake yanke hukuncin, Mai shari’a Ibrahim Musa-Muhammad ya ce wadanda suka shigar da karar sun kafa hujja da su.
Sanarwa cewa hana waɗannan kason zai kai ga tauye haƙƙoƙin al’ummar karkashin su da suke mulka cikin ƙananan hukumomi 44, kamar yadda aka tabbatar a ƙarƙashin sashe na 33, 42 da 43, 44, 45 da 46 na kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya na 1999 (wanda aka yiwa gyara).













































