Kasar Sweden ta dawo da bakin haure ‘yan Najeriya 36 da suka hada da kananan yara daga kasar.
Jami’an hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta kasa (NCFRMI) sune suka tarbi bakin hauren a ranar Laraba 8 ga watan Nuwambar da muke ciki a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe dake Abuja.
An dawo da ‘yan gudun hijirar ne karkashin shirin taimakon komawa gida na kasashen duniya wato IRARA.
Bayan dawowar su, an kuma basu wasu kayayyaki masu muhimmanci na mafanin yau da kullum da kuma kudi Naira dubu dari da hamsin da takwas (158,000) kowannen su.
Darakta mai kula da bakin haure ta hukumar, Ambasada Catherine Udida, ta bayyana cewa a mafi yawan lokuta ana ajiye bakin hauren na tsawon makonni biyu har zuwa shekara guda sannan kuma a tabbatar an ba su tallafin rayuwa.
Daya daga cikinsu da ta amince ta yi magana da manema labarai tare da boye sunan ta, ta ce jami’an shige da fice na kasar Sweden sun taso keyarta tare da duka daga cikin gidanta har zuwa filin jirgin sama.
Wasu kuma sun bayyana cewa su ba masu laifi ba ne, sun kuma zargi gwamnatin Sweden din da abin da suka kira zalunci.













































