Jam’iyyar APC ta fitar da cikakken jadawalin ayyuka na zaɓukan gundumomi, ƙananan hukumomi, jihohi da yankuna na ƙasa baki ɗaya na shekarun 2025 da 2026, waɗanda za su kai ga gudanar da babban taron jam’iyyar na ƙasa.
Sakataren jam’iyyar APC na ƙasa, Sanata Ajibola Bashiru, ne ya fitar da jadawalin ta shafinsa na X wanda a baya ake kira Twitter ranar Asabar.
Basiru ya ce jadawalin ya nuna cewa an tsara ayyukan bisa tanade-tanaden sashe na 11 da na 17 na kundin tsarin jam’iyyar APC domin zaɓen shugabannin jam’iyya a dukkan matakai.
Jadawalin ya nuna cewa za a fara da rajistar membobi ta hanyar na’ura daga ranar 1 ga watan Disamba 2025 zuwa 30 ga watan Janairu 2026, sannan a biyo da hakan da aika sanarwar tarukan zaɓe zuwa rassan jam’iyyar na jihohi da Babban Birnin Tarayya a ranar 2 ga watan Fabrairu 2026.
Haka kuma, saye da miƙa takardun tsayawa takara na gundumomi da ƙananan hukumomi za su gudana daga 4 zuwa 9 ga watan Fabrairu 2026, yayin da za a kafa kwamitocin tantance ‘yan takara a ranar 10 ga watan Fabrairu, sannan tantancewar ‘yan takarar za ta gudana daga 11 zuwa 13 ga watan Fabrairu.
Karanta: Tururuwa wajen sauya sheƙa zuwa APC: Tinubu yana kan hanya madaidaiciya – Abdulaziz Abdulaziz
An kayyade taron zaɓen gundumomi a ranar 18 ga watan Fabrairu 2026, tare da sauraron ƙorafe-ƙorafen da suka taso a ranar 19, yayin da taron ƙananan hukumomi, ciki har da zaɓen wakilai uku zuwa babban taron jam’iyyar na ƙasa inda dole ɗaya ta kasance mace, za su gudana a ranar 20 ga watan Fabrairu, sannan a saurari ƙorafe-ƙorafe a ranar 21.
A matakin jihohi, saye da miƙa takardun tsayawa takara na shugabannin jiha za su fara daga 23 zuwa 27 ga watan Fabrairu 2026, yayin da taron jihohi zai gudana a ranar 7 ga watan Maris 2026.
Sannan daga bisani a koma matakin yankuna inda tarukan yankuna za su gudana a ranar 21 ga watan Maris 2026, kafin a kammala da babban taron APC na ƙasa da aka shirya gudanarwa daga 25 zuwa 28 ga watan Maris 2026.













































