Idan zanga-zanga ta ƙazance to fa za mu ɗau mataki — Sojoji

CDS

Babban Hafsan Tsaro (CDS), Christopher Musa, ya ce sojoji za su shigo ciki idan zanga-zangar ‘#EndbadGovernance’ da ke ci gaba da gudana a fadin kasar ta ci gaba da rikide wa zuwa tashin hankali.

Musa dai na mayar da martani ne kan barna da sace-sace da aka yi a zanga-zangar da aka yi a sassa da dama na kasar a jiya Alhamis.

Ko a jiyan ma sai da aka farfasa cibiyar sadarwa ta musamman ta NCC a Kano, inda aka sace kayaiyaki na biliyoyin Naira.

Da yake zantawa da manema labarai a yau Juma’a, Musa ya bukaci masu zanga-zangar da su gane cewa barna ba ta da amfani kuma zai jefa al’ummar kasar cikin rudani.

Yayin da yake yabawa rundunar ƴansandan Najeriya bisa kokarin da take yi na tabbatar da zaman lafiya, ya kara da cewa za a tilastawa sojoji shiga lamarin idan har aka ci gaba da samun tashin hankali.

Ya ce: “Ya kamata mu gane cewa wadannan barna da kudaden mu aka samar da su kuma da kudaden mu za a gyara su idan kuka bata.

“Don haka maimakon yin haka, ya kamata mu hada kai don tabbatar da cewa babu wani abu. ya lalace,” in ji shi.

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here