Hukumar yaƙi da cin hanci da sauran laifuka masu alaƙa da su ta ICPC ta gurfanar da Amadu Sule, wanda shi ne babban daraktan kamfanin TMDK Terminal Limited kuma abokin tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, kan zargin hannu a shirin wanke kuɗaɗen da adadinsu ya kai naira biliyan 311.
An gurfanar da Amadu Sule a gaban babbar kotun tarayya da ke Kaduna, inda aka gabatar masa da tuhume-tuhume guda biyar da suka shafi wankiyar kuɗaɗe da kuma riƙe kuɗaɗen da ake zargin an samo su ta hanyar damfara, wanda ya saɓa da dokar hana wanke kuɗaɗe ta shekarar 2022.
Takardun tuhumar da hukumar ICPC ta gabatar sun nuna cewa Amadu Sule ya mallaki iko da sarrafa fiye da Naira Biliyan 311 da aka gano suna shiga asusu a bankuna uku daban-daban.
Bayanai sun nuna cewa kuɗaɗen sun fito ne daga kamfanonin INT Towers Limited, IHS Nigeria Limited, IHS Towers NG Limited da Boaz Commodities Limited, inda aka bayyana cewa an biya su ne bisa hujjar samar da kayayyakin man fetur.
Hukumar ICPC ta nuna cewa ya dace Amadu Sule ya fahimci cewa kuɗaɗen da aka shigar cikin asusun sun samo asali ne daga ayyukan da ba su halasta ba.
Haka kuma, hukumar ta bayyana cewa Amadu Sule da kamfanin TMDK Terminal Limited sun riƙe kuɗaɗen haraji da suka shafi mu’amalolin da ake takaddama a kansu, waɗanda adadinsu ya kai daruruwan Biliyoyin Naira, duk da kasancewar suna sane da cewa mu’amalolin asali na yaudara ne.
Hukumar ta bayyana waɗannan ayyuka a matsayin sarrafawa da kuma riƙe kuɗaɗe haramtattu kai tsaye, lamarin da ke fallasa mutum da kamfanin ga hukunci mai tsanani a ƙarƙashin sashe na 18(3) da 18(4) na dokar.
Shari’ar ta jawo hankalin jama’a saboda alaƙar kasuwanci da siyasa da kamfanin TMDK Terminal Limited ke da ita da iyalan El-Rufai, ciki har da tsohon gwamnan Jihar Kaduna da kuma ɗan uwansa babba Bashir El-Rufai, waɗanda ake ganin sun yi mu’amala da kamfanin a lokacin mulkinsa da bayan saukarsa daga mulki.
Amadu Sule ya musanta dukkan tuhume-tuhumen da aka karanta masa, inda kotu ta ɗage shari’ar zuwa ranar da za a saurari buƙatar belinsa.













































