Hukumar Yaki da Cin Hanci da sauran laifuffuka ta kasa (ICPC), ta ce za ta gurfanar da ‘yan kwangilar da suka gaza gudanar da ayyukan mazabu a jihar Kano.
Babban mataimakin sufirtandan ofishin ICPC na Kano, Bukar Galadima ne ya bayyana wa Solacebase hakan a ranar Asabar, yayin gudanar da wani zagaye na bin diddigin ayyukan mazabu a makarantar firamare ta Zogarawa dake karamar hukumar Dawakin Kudu, wadda ke karkashin Sanata mai wakiltar Kano ta tsakiya.
Karanta Wannan: Al’ajabi: Wani Dalibin Kwalejin Kimiyya Da Kere-Kere Ya Rataye Kansa
Solacebase ta ruwaito cewa, shugaban tawagar ICPC na Kano, Bukar Galadima, ya ce galibin ayyukan mazaba dake karkashin Sanata mai wakiltar Kano ta tsakiya, an same su da tangarda kuma ba a gudanar da su bisa ka’idar kwangilar ba.
”Za mu gurfanar da dukkan ‘yan kwangilar da zarar mun kammala binciken mu”, in ji Galadima.
A cewarsa ”Dukkan ayyukan makarantun firamare dake ƙarƙashin mazabar, wadanda aka ce an kammala su a 2020, an same su da rashin inganci, mafi yawa rufinsu da fenti sun lalace kuma babu kujeru. ”
Idan za a iya tunawa kwanan nan ICPC ta ziyarci wasu ayyukan mazabu a shiyyar sanatan Kano ta tsakiya a wasu ƙananan hukumomin da suka haɗa da, Warawa, Dawakin Kudu, Tarauni, Kano Municipal, da Dala.
A cewar shugaban tawagar, ci gaba da bin diddigin ayyukan mazabu da hukumar ke yi a Kano da sauran jihohin Tarayyar, ba sa nufin cin dunduniyar wani dan siyasa ko wani mutum, sai dai don tabbatar da al’umma sun ci moriyar ayyukan kamar yadda suke.
Karanta Wannan:‘Yan Sanda Sun Ceto Basaraken Da Aka Yi Garkuwa Da Shi a Jihar Niger
Ya ce bin diddigin ayyukan abu ne mai mahimmanci ga ICPC sakamakon yadda kasar ta kashe biliyoyin nairori tun daga shekarar 2000, ba tare da samun ci gaban da ya dace a matakin farko ba.















































