Gwamnatin tarayya ta shiga tsakani a rikicin da ke tsakanin ƙungiyar ma’aikatan Mai da iskar Gas (NUPENG) da kamfanin Dangote, inda ta roƙi ƙungiyar da ta janye shirin fara yajin aikin gama gari a fadin ƙasa daga Litinin, 8 ga Satumba, 2025.
Ministan Ƙwadago da ayyukan yi, Muhammad Maigari Dingyadi, ya tabbatar a ranar Lahadi cewa ya gayyaci dukkan ɓangarorin da abin ya shafa zuwa taron sulhu a Abuja.
Wannan mataki ya biyo bayan zargin cewa Dangote na hana ma’aikatansa shiga ƙungiyoyin kwadago.
Labari mai alaƙa: Ƙungiyar Direbobin Tankar Mai ta buƙaci direbobi su yi watsi da sanarwar yajin aikin NUPENG
A cewar sanarwar da Ma’aikatar ta fitar ta bakin shugabar yada labarai, Patience Onuobia, Ministan ya roƙi NUPENG da ta dakatar da yunkurin tsayar da ayyukan man fetur, tare da kira ga ƙungiyar ƙwadago ta Ƙasa (NLC) da ta janye umarnin da ta bai wa rassanta na goyon bayan ma’aikatan mai.
Dingyadi ya yi gargadin cewa yajin aikin man fetur zai jefa ƙasa cikin matsanancin halin rayuwa tare da janyo asarar kuɗaɗen shiga ga gwamnati.
Ya ce: “Sashen man fetur muhimmin ginshiƙi ne ga tattalin arzikin ƙasa. Ko da kwana guda aka yi yajin aiki, asarar da za a yi za ta kai biliyoyin naira, kuma talakawa za su shiga cikin ƙuncin rayuwa.”
Ya ƙara da cewa gwamnati za ta tabbatar da zaman lafiya da cimma matsaya da za ta amfanar da dukkan ɓangarorin da abin ya shafa. “Za mu sasanta lamarin cikin ruwan sanyi don tabbatar da amincewa daga bangarorin biyu,” in ji Ministan.













































