Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin Abdulganiyu Jaji a matsayin sabon shugaban hukumar kashe gobara ta tarayya, daga ranar 22 ga Afrilun shekarar 2022.
Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Aisha Rufa’I, sakatariyar hukumar kula da ma’aikatun tsaron farin kaya da shige da fice da kuma gidajen ajiya da gyaran hali (wato CDIPB) ranar Talata, a Abuja.
Kamfanin Dillancin Labarai NAN ya rawaito cewa kafin a nada Jaji, matsayin shugaban hukumar ya kasance mataimakin shugaban mai kula da harkokin mulki a hukumar.
Ya karbi mukamin ne daga hannun Mukaddashin Kwanturola Janar Samson Karebo, wanda ya karbi ragamar shugabancin hukumar bayan da tsohon Konturola Janar Ibrahim Liman ya yi ritaya.
Rahotanni sun bayyana cewa, sabon Kwanturolan da aka nada ya fara aikinsa ne a ma’aikatar ayyuka da gidaje ta tarayya a matsayin babban jami’in fasaha tun a shekarar 1991.
“Ya rike mukamai da dama a ma’aikatar kafin ya sauya wajen aiki zuwa hukumar kashe gobara ta tarayya a shekarar 1999.
“An haife shi a ranar 13 ga Agusta na shekarar 1965 a Ilorin, Jihar Kwara.
“Ya yi Digiri na biyu a fannin Mechanical Engineering a shekarar 1999 kuma yana da aure da ‘ya’ya.”













































