Gwamnatin tarayya da ASUU za su kammala yarjejeniya kan ƙarfafa tsarin jami’o’i

ASUU vs Federal Government 1

Gwamnatin tarayya da ƙungiyar malaman jami’o’i ta ƙasa ASUU na shirin kammala wata babbar yarjejeniya da aka riga aka sanya wa hannu, domin ƙarfafa zaman lafiyar aiki da inganta yanayin koyarwa da koyo a jami’o’in Najeriya.

Yarjejeniyar ta kuma mayar da hankali ne kan bunƙasa ci gaba mai dorewa a tsarin jami’o’in ƙasar, ta hanyar samar da yanayi mai inganci da zai taimaka wajen haɓaka ilimi da bincike.

Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da daraktar yaɗa labarai da hulɗa da jama’a ta ma’aikatar ilimi ta tarayya, Folasade Boriowo, ta fitar ga manema labarai a birnin Abuja.

Sanarwar ta nuna cewa za a gudanar da bikin kaddamar da yarjejeniyar a ranar Laraba, 14 ga watan Janairu, a Abuja, domin tabbatar da aiwatar da abubuwan da aka cimma matsaya a kai.

Bikin zai gudana ne a ƙarƙashin jagorancin ministan ilimi, Dakta Tunji Alausa, tare da ministar ƙasa a ma’aikatar ilimi, Farfesa Suwaiba Ahmad, inda za su wakilci gwamnatin tarayya a wajen taron.

Ci gaban ya yi daidai da ajandar Sabunta Manufa na Shugaban ƙasa Bola Tinubu, wadda ke ɗaukar ilimi a matsayin muhimmin ginshiƙi na ci gaban ƙasa, bunƙasar ƙwarewar ɗan Adam da sauyin tattalin arziki da zamantakewa.

Sanarwar ta jaddada cewa yarjejeniyar za ta taimaka wajen ƙarfafa zaman lafiya a tsakanin jami’o’in Najeriya, samar da yanayi mai kyau na karatu da aiki, tare da ƙara amincewa a tsakanin ɗalibai, ma’aikata da al’umma gaba ɗaya.

NAN

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here