Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta tabbatar da tashin gobara a safiyar Laraba da ta kone ofisoshi 17 a sakatariyar karamar hukumar Gwale.
Jami’in hulda da jama’a na hukumar, Saminu Abdullahi, shi ne ya tabbatar da faruwar lamarin a zantawar sa da kamfanin dillancin labaran Najeriya a Kano.
Abdullahi ya ce ginin da ake amfani da shi a matsayin ofisoshi mai tsawon mita 300 da fadin kafa 200 ya kone gaba daya.

Karanta wannan:Ilimin Yara Mata: Sarkin Katsina ya yi barazanar soke shirin AGILE a fadin Jihar
Ya kuma ce akwai motoci kirar Peugeot 406 da Haice guda daya da motar daukar marasa lafiya suma sun kone.
Ya ce yanzu haka hukumar na binciken musabbabin tashin gobarar.












































