Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta bayyana dalilin da ya sa ‘yan sanda suka cafke tsohon kwamishinan ayyuka da samar da ababen more rayuwa na jihar Kano, Muaz Magaji.
Mista Magaji, mai tsananin adawa da gwamna Ganduje, ‘yan sanda sun kama shi ne a Abuja jim kadan bayan da aka yi hira da shi kai tsaye a gidan talabijin na Trust da ke Utako.
Nan take aka kai shi Kano, kuma ya kwana a hedikwatar rundunar da ke Bompai.
Da yake zantawa da DAILY NIGERIAN a ranar Juma’a, mai magana da yawun rundunar, Abdullahi Kiyawa, ya ce ‘yan sandan sun kama shi ne bayan da ya ki mika kan sa ga ‘yan sanda domin amsa tambayoyi duk da gayyatar da aka yi masa.
ASP Kiyawa, ya ce ‘yan sandan sun gayyace shi, bisa umarnin kotu na a binciki shi.
“A halin yanzu muna kan binciken tuhume-tuhume da suka hada da bata sunan mutum, cin mutunci da gangan, karya da kuma tayar da hankali ga Muaz Magaji,” in ji kakakin ‘yan sandan.
Binciken DAILY NIGERIAN ya nuna cewa gwamna Ganduje da kan sa ya umurci lauyoyinsa, Adekunle Taiye Falola & Co. da su kai karar Mista Magaji a wata kotun majistare da ke Kano.
Sakamakon binciken ya nuna cewa an mika karar ne ga alkalin kotun majistare mai lamba 58, Nomansland, Aminu Gabari.
Majiyar rundunar ‘yan sandan ta ce za a gurfanar da Mista Magaji gaban kotu a yau.












































