An zabi babban Daraktan gudanarwa na Cibiyar Noma ta busasshiyar Kasa (CDA) Dake Jami’ar Bayero Kano Farfesa Jibrin Mohammed Jibrin a matsayin shugaban cibiyar samar da abinci ta yammacin Afirka.
Jaridar Solacebase ta rawaito cewa FOOD4WA wata cibiya ce daga cikin cibiyoyin noma ta Africa wacce ta hada cibiyoyi bakwai daga kasashen Afirka shida wadanda ayyukansu suka mayar da hankali kan noma, samar da abinci da abinci mai gina jiki.
A halin yanzu cibiyar tana aiki don ƙarfafa ƙwarewa da horar da matasan Afirka waɗanda za su iya ɗaukar ƙalubalen wadatar da abinci, da abinci mai gina jiki.
Rahotanni sun ce jami’o’in da ke karbar bakuncin Cibiyoyin za su hada kai da ‘yan uwa jami’o’i don musayar ilimi da inganta motsin dalibai da malamai a Afirka.
Cibiyar a cikin watan Agusta 2022 ta shirya taron ta na farko wanda Cibiyar Inganta Aikin Noma ta Afirka dasuka hadar da Jami’ar Cheikh Anta Diop dake Dakar, Senegal ta shirya.
Farfesa Jibrin ya gaji Farfesa Kokou Tona, Shugaban Cibiyar Kwarewa kan har noma ta Afirka na Jami’ar Lomé, dake Ƙasar Togo.