Buhari ya roƙi ‘yan Najeriya su sakawa gwamnatin Tinubu albarka

Buhari, tshohon, shugaban, kasa, tinubu, najeriya, albarka
Tsohon Shugaban Kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya taya Shugaban Ƙasa Bola Tinubu murnar cika shekara ɗaya a kan mulki, yana mai neman 'yan ƙasar su goyawa...

Daga: Sunusi A. Dantalata Fagge

Tsohon Shugaban Kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya taya Shugaban Ƙasa Bola Tinubu murnar cika shekara ɗaya a kan mulki, yana mai neman ‘yan ƙasar su goyawa gwamnatin jam’iyyarsu ta APC baya don ta yi nasara wajen gina ƙasa.

Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun tsohon shugaban ya wallafa a shafukan zumunta, Buhari ya kuma nemi ‘yan Najeriya su saka wa gwamnatin ta Tinubu albarka kuma su ƙara ƙarfafa haɗin kan ƙasa.

Karin labari: Rigimar Masarauta: Gwamnan Kano ya bada umarnin kama masu yin taruka da zanga-zanga dana Dalibai

Haka nan, Buhari ya yiwa gwamnatin Tinubu fatan gama mulki cikin nasara,” in ji Garba Shehu.

A yau Laraba 29 ga watan Mayu Tinubu ke cika shekara ɗaya da shan rantsuwar kama mulki bayan ya yi nasarar lashe zaɓen shugaban ƙasa a zaɓen watan Fabrairun 2023 a ƙarƙashin jam’iyyar APC.

Muhammadu Buhari ne shugaban ƙasar da ya fara cin zaɓe a APC, inda ya mulki ƙasar daga 2015 zuwa 2023.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here