Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana kaduwar sa bisa rahoton sace jarirai biyar da aka haifa a Anambra, inda ya bayar da umarnin rage yawan laifuka a yankin ba tare da ɓata lokaci ba.
An yi garkuwa da jariran ne a asibitin Stanley da ke Nkpologwu a jihar.
An ce masu garkuwa da mutanen sun sato jariran ne kuma su ka tsere a abin-hawa.
A wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Garba Shehu ya fitar a yau Juma’a a Abuja, Buhari ya bayyana damuwar sa game da wannan abinda ya kira bakon lamari, inda ya ce dole a gaggauta magance wannan matsalar.
Don haka, ya ba da umarnin, “Tsaro a asibitoci ya zama dole don kada hare-hare irin wannan ya sake faruwa.”