An yi musayar yawu tsakanin NNPP da APC a kano bisa zargin raunata magoya baya

NNPP APC 750x430 1
NNPP APC 750x430 1

Jam’iyyar NNPP ta koka bisa hare-haren da ake zargin wasu ‘ya’yan jam’iyyar APC na jihar Kano na kai wa mambobinta.

Shugaban jam’iyyar NNPP na Kano Umar Haruna Doguwa, ne ya yi wannan zargin a wani taron manema labarai da aka gudanar a sakatariyar jam’iyyar a karshen mako.

Doguwa ya koka da yadda wasu da ake zargin ’yan APC da suka hada da: Abba Dagi, Junaidu da Shehi karkashin jagorancin Sani Abdullahi Abas wanda aka fi sani da Orchi da ake zargin sun kai hari Chiranchi tare da raunata da yawa daga cikin mambobinta a karamar hukumar Gwale.

Doguwa ya ce an sanar da su cewa jam’iyyar APC a karkashin jagorancin shugaban jihar, Alhaji Abdullahi Abbas ta yi taro a ranar Asabar, inda ake zargin an yanke shawarar zafafa hare-haren da ake kaiwa mutanen da ba su ji ba ba su gani ba, da sauran ‘yan jam’iyyar siyasa musamman NNPP, domin ganin an shawo kan lamarin.

Ya yi kira ga sabon kwamishinan ‘yan sanda, Mamman Dauda da ya gargadi jami’an da ya ce suna da hannu a cikin lamarin.

Da yake mayar da martani kan zargin, Shugaban APC na Kano, Abdullahi Abbas, ya musanta gudanar da wani taro da nufin haifar da rikici domin kada a gudanar da babban zabe a jihar.

”Wannan zargin abin dariya ne, domin mu da muke da yakinin lashe zaben badi, to don me ya sa za mu so mu hana gudanar da zabe, ”in ji Abbas.

Da jaridar Solacebase ta tuntubi Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, kan zargin da NNPP ke yi wa DPO na Gwale da Mandawari, ya bukaci a ba shi lokaci kadan dan buncikar halin da ake ciki.

Kiyawa ya kara da cewa, ”Kun ga sabon kwamishinan ‘yan sandan da aka nada ya sa ya zama al’adar zagayawa cikin gari da kansa don sa ido da kuma lura da halin da ake ciki don tabbatar da lokacin gudanar da zabe cikin lumana.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here