An saki tsohon ministan Shari’a Malami bayan amsa tambayoyi daga EFCC

Abubakar Malami

Tsohon babban lauya na ƙasa kuma ministan shari’a, Abubakar Malami (SAN), ya bayyana cewa zaman da ya yi da Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa EFCC bayan an gayyace shi don tambayoyi ya ƙare cikin nasara.

A wani saƙo da ya wallafa a shafin sa na X a safiyar Asabar, Malami ya tabbatar da cewa an saki shi kuma an tsara wani zaman tare da masu bincike.

Ya jaddada cewa gaskiyar abin da ake zarginsa da shi, wanda ya kira “zargin ƙarya,” za ta bayyana a fili da zarar lokaci ya yi.

Ya ce, a bisa alkawari na sanar da ‘yan Najeriya game da gayyata ta daga EFCC, ina gode wa Allah bisa taimakon sa.

Labari mai alaƙa: Tsohon babban Lauya gwamnati Abubakar Malami ya tabbatar da amsa gayyatar hukumar EFCC

“Zaman ya kasance cikin nasara, kuma an sake ni yayin da aka tsara wani zama na gaba domin ci gaba da bincike, yayin da gaskiyar da ta shafi zargin ƙarya da aka yi min ke fitowa.” in ji malami.

Tsohon ministan shari’a ya ce an gayyace shi ne don ya amsa tambayoyi kan wasu zarge-zarge da ake masa a lokacin da yake kan mulki.

Ya kara da cewa, a shirye yake ya bi umarnin EFCC gaba ɗaya, a matsayin alamar gaskiya da shugabanci mai ɗaukar alhaki, yana mai cewa wannan tsayuwar daka ta shi ta dace da ka’idojin da ya tsaya a kai a lokacin da yake kan mulki.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here