An sake zabar dan majalisa mai wakiltar mazabar Agege na daya, Mudashiru Obasa a matsayin shugaban majalisar dokokin jihar Legas.
A ranar Litinin ne aka sake zaben Obasa bayan murabus din Mojisola Meranda wadda ta ajiye mukamin kakakin majalisar.
Sake zabensa ya biyo bayan nadin da tsohon shugaban masu rinjaye a majalisar, Noheem Adams, mai wakiltar mazabar Eti-Osa 1 ya yi.
Daga bisani Obasa ya sha rantsuwa na sake zama sabon shugaban majalisar dokokin jihar Legas makonni bakwai bayan tsige shi.
Karanta: Majalisar Legas: Tsohon shugaban majalisar Obasa ya jagoranci zama da mambobi 4
An fara zaben shi a majalisar ne a shekarar 2007, kuma ya kasance a zauren majalisar tun lokacin, har zuwa matakin shugaban majalisar a watan Yunin 2015 kafin a cire shi a watan Janairun 2025.
Sai dai rikicin shugabanci a majalisar ya yi kamari ne a ranar 13 ga watan Janairun 2025, lokacin da aka tsige dan majalisa mai wakiltar mazabar Agege na daya, Mudashiru Obasa daga mukamin kakakin majalisar Legas sama da kashi biyu bisa uku na mambobi 40 da suka kada kuri’a kan amincewa da zargin sa da rashin da’a da kuma laifuka daban-daban.
Nan take aka zabi mataimakiyarsa Meranda, a matsayin sabuwar kakakin majalisar, inda ta zama mace ta farko da ta karbi ragamar majalisar a jihar ta Kudu-maso-Yamma.
A ranar 25 ga Janairu, 2025, Obasa ya ki amincewa da tsige shi, inda ya ci gaba da zama shugaban majalisar har sai an yi abin da ya dace, saboda an tsige shi lokacin da ba ya kasar.