An kashe fararen hula kusan 200 a rikicin Sudan

342021762 3568924420031875 8825079842617031532 n
342021762 3568924420031875 8825079842617031532 n

Likitoci a Sudan sun ce kusan farar hula 200 ne suka mutu, wasu ɗaruruwa suka jikkata, yayin da asibitoci a birnin Khartoum ke ci gaba da fama da ƙarancin kayan aiki.

Shi ma, Babban jami’in Tarayyar Turai kan manufofin ƙasashen ketare, ya ce an kai wa Jakadan tarayyar Turai, Aidan O’Hara a Sudan hari a gidansa da ke birnin Khartom.

Josep Borrell ya wallafa a shafin sada zumunta, cewa hakkin kula da jakadan da muhallinsa ya rataya a wuyan hukumomin Sudan, inda ya tabbatar da cewa jakadan na cikin koshin lafiya.

Ya ce ɗaya daga cikin abin da ya bayyana karara tun bayan ɓarkewar rikicin shi ne daga Hameti har Burhan ba su nuna alamun za su aminta da dakatar da buɗe wuta ba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here