Dan wasan tsakiya na Najeriya, Alhassan Ibrahim, ya kammala komawa kungiyar kwallon kafa ta KVA Beerschot dake kasar Belgium.
Tsohon Dan wasan tawagar Akwa United, da Wikki Tourist, Ibrahim, ya rattaba hannu kan yarjejeniyar shekaru biyu da sabuwar tawagar ta sa.
Haka zalika Dan wasan ya sauya sheka ne daga kungiyar kwallon kafa ta CD Nacional ta Kasar Portugal da ya taka Leda a baya.
Mai shekaru 25 Mu’azzam, ya koma Kungiyar Austria Vienna ta Kasar Austria a shekarar 2017, kafin ya sauya sheka zuwa kasar Portugal.













































