Gwamnatin jihar Zamfara ta ce ta kama motocin da ke kai kayan abinci, da abin sha da man fetur zuwa sansanin ‘yan fashi da ke jihar.
Gwamnatin ta ce ta kuma kama akalla mutane 100 da suka karya dokar Gwamna Bello Matawalle don tabbatar da doka da oda a jihar.
Sakataren runduna ta musamman kan tsaro, Mista Abdulrasheed Haruna, ne ya bayyana wa Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) hakam a Gusau ranar Laraba.
Matawalle ya kafa runduna ta musamman don aiwatar da matakan da za su magance matsalolin tsaro da ke addabar garkuwa da mutane don neman kudin fansa da satar shanu da ‘yan bindiga ke yi a jihar.
Idan za a iya tunawa Solacebase ta ruwaito cewa Matawalle ya sanya hannu a kan wani umarni a ranar 26 ga watan Agusta, na magance matsalolin tsaro.
Da yake rattaba hannu kan umarnin, gwamnan ya ce ya yi aiki da ikon da Sashe na 5 (2), 176 (2) da 315 (2) na Kundin Tsarin Mulkin 1999 na Tarayyar Najeriya suka bashi.
Ya kuma ce yana aiwatar da dukkan sauran karfin da ke ba shi damar a wannan matsayin a kokarin kare rayuka da dukiyoyin jama’ar jihar Zamfara wadda ke tattare da kalubalen tsaro.










































