Da ɗumi-ɗumi: INEC ta ƙara wa’adin kammala zaɓen fidda gwani

INEC Mahmood 1
INEC Mahmood 1

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Najeriya INEC, ta ƙara wa jam’iyyu lokacin kammala zaɓukan fitar da gwani na zaɓen 2023.

Shugaban kwamitin yaɗa labarai da wayar da kan masu kaɗa kuri’a Festus Okoye ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da ya fitar yau Juma’a a Abuja.

Sanarwar ta ce: Hukumar zaɓe mai zaman kanta INEC ta gana da shugabannin jam’iyyun siyasa a yau Juma’a 27 ga watan Mayu 2022, jam’iyyun sun buƙaci hukumar da ta sake duba lokutan gudanar da zaben fidda gwanin jam’iyyun wanda ke cikin jadawalin ayyukan da za a gudanar a zaɓen 2023 da aka fitar ranar Asabar 26 ga Faburairun baɗi.

Sai dai a bisa jadawalin ayyukan babban zaben 2023, yanzu jam’iyyun sun roki hukumar da ta yi amfani da wa’adin kwanaki 6 tsakanin 4 zuwa 9 ga watan Yunin ban don kammala zaɓukan fidda gwanin.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here