Kwamitin Zartarwa na Kasa ba shi da hurumin dakatar da Dalhatu – Kwamitin Amintattu

Dalhatu 750x430

Kungiyar Tuntuba ta Arewa (ACF), ta bayyana cewa a cikin kwanaki masu zuwa za ta magance rikicin shugabanci da ya kai ga ‘yan sanda sun rufe hedkwatar kungiyar ta kasa a ranar Talata da ta gabata.

A cikin wata sanarwa da Kwamitin Amintattu ya fitar kuma aka amince da ita ta hannun wasu manyan mambobi, ACF BoT ta ki amincewa da dakatar da Shugabanta, Alhaji Bashir M. Dalhatu, da Kwamitin Zartarwa na Kasa (NEC) na kungiyar karkashin jagorancin Shugabanta, Mike Mamman Osuman, SAN, ya yi.

SolaceBase ta ruwaito cewa daga cikin wadanda suka sanya hannu kan sanarwar akwai Hassan Adamu, Muhammad Maigoro, A.M. Haruna, tsohon SGF Yayale Ahmed, Yusuf Buratai, Solomon Dalung, tsohon IGP M.D. Abubakar, Ibrahim Shekarau, Abdullahi Adamu da Sule Lamido.

A cewar sanarwar, “Kwamitin Amintattu (BoT) ya sake tabbatar da amincewa da goyon bayan ga Shugaban kwamitin, Alhaji Bashir Mohammed Dalhatu, cikin kwanaki masu zuwa, za mu dauki matakai da suka dace da za su magance wannan rikici maras amfani da sake dawo da ladabtarwa, zaman lafiya da tsari a cikin wannan kungiya mai matukar muhimmanci.”

“Kwamitin Amintattu na (ACF) ya yi Allah wadai da aiki, rashin natsuwa, kan ayyukan da ba su da amfanin, ba bisa ka’ida ba da na rashin taka tsantsan da wasu mutane ‘yan kalilan ke aikata wa a cikin kungiyar, wadanda suka saba wa Kundin Tsarin Mulkin kungiyar dokoki, ka’idoji, al’adu da dabi’u, suka kira taro maras inganci a ranar 6 ga Mayu, 2026, kuma suka fitar da sanarwar manema labarai da ke dauke da zarge-zarge marasa tushe da mugunta kan mutum mai mutunci, Shugaban Kwamitin Amintattu, Alhaji Bashir Dalhatu, Wazirin Dutse.”

“Saboda kauce wa shakku, Kwamitin Zartarwa na Kasa (NEC) ba shi da wani hurumi na doka na yanke hukunci kan shugabancin Kwamitin Amintattu, ba shi da hurumi a karkashin kundin tsarin mulkinmu na nadawa, dakatarwa ko korar kowane memba na Kwamitin Amintattu, balle Shugabansa. Ayyukan wadannan tsirarun mambobin hadari na rashin ladabtarwa, rashin biyayya da kokari a bayyana na raunana tushen kungiyar.”

Sanarwar ta kara da cewa, “Abin takaici ne kuma abin damuwa cewa Shugaban Kwamitin Zartarwa na Kasa, Mike Mamman Osman, SAN, ya amince da ayyukan da ba su da inganci na tsohon Sakatare Janar, Murtala Aliyu, wanda wa’adinsa ya kare a ranar 10 ga Maris, 2026. Duk wani aiki da tsohon Sakatare Janar din ya yi bayan wannan kwanan wata ba shi da inganci, kuma babu tasiri. An kuma fara bincike a kansa kan halayensa yayin da yake kan mukami.”

Sanarwar ta kara da cewa, “Kwamitin Amintattu ya ba da umarnin gudanar da bincike kan abin da ya haifar da wannan cin amanar, wanda babu shakka an shirya shi ne domin bata wa kungiyar suna, wulakanta mutuncinta dawo da ita baya.

“Muna so mu bayyana a gili cewa babu rikicin shugabanci ko fafatawa a cikin Kungiyar Tuntuba ta Arewa, abin da muke gani ba komai ba ne face shirye-shiryen mugunta da son kai na tsohon jami’i wanda ya ki barin mukaminsa bayan kare wa’adinsa, kuma ya dauki wasu mutane kalilan masu irin tunaninsa domin su yi masa abin da yake so,” in ji Kwamitin.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here