Kwamitin Hadin Gwiwa (JAC) na ma’aikatan jami’o’i da ba malamai ba, ya ce za a dakatar da yajin aikin da ake yi a faɗin kasar nan ranar Litinin.
JAC ta kunshi Kungiyar Ma’aikatan da ba Malamai da Kungiyoyi Ilimi (NASU) da Kungiyar Manyan Ma’aikata Jami’o’in Najeriya (SSANU).
Gamayyar kungiyoyin sun bayyana matsayar ne a cikin wata sanarwa da Mista Peters Adeyemi, Sakatare Janar na NASU, da Mista Mohammed Ibrahim, Shugaban SSANU, suka fitar a Abuja a ranar Laraba.
An aika sanarwar ga dukkan shugabannin rassan NASU da SSANU a jami’o’i da cibiyoyin jami’o’i a fadin ƙasar.
Kwamitin ya kuma bayyaba cewa kungiyoyin sun gudanar da taruka da dama da jami’an gwamnati tun lokacin da yajin aikin ya fara a 1 ga Mayu, 2026.
“Kwamitin ya amince da alkawarin gwamnati na cewa za a kammala tattaunawar sake fasalin yarjejeniya, ciki har da bitar CONTTA, cikin makonni biyu.
“Shugabannin rassan ana kiransu da su bi wannan rokon su gudanar da taruka na mambobi domin bayar da rahoto kan haka, don dakatar da yajin aikin, wanda zai fara aiki daga Litinin 11 ga Mayun shekarar 2026, yayin da sauran tattaunawa da masu ruwa da tsaki ke ci gaba,” in ji sanarwar.
JAC ta kuma amince da karbar wasikun rokk daga Kwamitin Sake Fasalin Ma’aikatan Manyan Cibiyoyin Ilimi da kuma janye kariin kashi 30 na CONTTA.
Kwamitin ya mika godiya ga dukkan mambobi kan cikakken biyayya yayin yajin aikin, tare da bukatar su ci gaba da baiwa kungiyoyin cikakken hadn kai. (NAN)










































