Datti Baba-Ahmed ya fice daga Labour Party ya koma PRP

Yusuf Datti Baba Ahmed 675x430

Tsohon dan takarar mataimakin shugaban kasa a jam’iyyar Labour Party a Najeriya, Yusuf Datti Baba-Ahmed, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar, yana mai bayyana cewa zai koma jam’iyyar PRP a hukumance cikin daren yau, 28 ga watan Afrilu.

Baba-Ahmed ya bayyana hakan ne a yammacin ranar Talata, yayin da ya bayyana a shirin Politics Today na gidan talabijin na Channels.

Ya bayyana rikice-rikicen cikin gida na jam’iyyar Labour Party da abin da ya bayyana a matsayin ficewa daga akidun da aka kafa ta a matsayin manyan dalilan ficewarsa.

“Jam’iyyar Labour Party ta yanzu, ba ita bace a da,”in ji shi, inda ya kara da cewa matsin lamba na siyasa da katsalandan daga waje sun taimaka wajen kawo rashin zaman lafiya a cikin jam’iyyar.

Baba-Ahmed ya cewa yanayin siyasar yanzu ya zama abu mai wahala ga jam’iyyun adawa su bunkasa, yana zargin cewa ana kokarin raunana su maimakon magance muhimman batutuwan kasa kamar rashin tsaro da wahalhalun tattalin arziki.

Ficewarsa ta zo ne a daidai lokacin da rikicin shugabanci ke kara muni a cikin jam’iyyar Labour Party, inda Nenadi Usman ta zama shugaba, lamarin da ya kara zurfafa rikicin bangaranci.

Baba-Ahmed ya bayyana PRP a matsayin jam’iyya mai kakkarfan tushe na tarihi kuma ya gabatar da ita a matsayin sabon dandalinsa na siyasa, yana nuna kyakkyawan fata cewa za ta iya samar da wani madadi mai inganci gabanin zabukan da ke tafe.

Wannan mataki na baya-bayan nan na nuna wani babban sauyi a fagen adawa a Najeriya, wanda ke tayar da sabbin tambayoyi game da zaman lafiya da makomar jam’iyyar Labour Party.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here