Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya sauke shugaban Ma’aikata Alhaji Abdullahi Musa, daga mukaminsa.
Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a daren Talatar makon nan ce ta bayyana hakan.
Sanarwar ta ce, ɗaukar matakin sauke shi ɗin na daga cikin Ƙoƙarin gwamnati na sake inganta aiki da kuma kyautata yadda hukumomin gwamnati ke gudanar da ayyukansu.
Gwamnan na Kano, ya kuma yaba wa tsohon Shugaban Ma’aikatan bisa gudunmawar da ya bayar da kuma jajircewarsa wajen yi wa Jihar Kano hidima a lokacin da ya ke kan mukamin.
Haka kuma ta cikin sanarwar, gwamna Abba, ya kuma yi masa fatan alheri da nasara a rayuwarsa ta gaba.
Sanarwar ta kara da cewa gwamnan ya umurci Hajiya Bilkisu Shehu Maimota, wadda ke matsayin Babbar Sakatariya mai kula da sashen gudanarwa da kuma ayyuka na musamman da ta rike muƙamin na Shugaba ma’aikatan Jiha na rikon kwarya, har sai zuwa lokacin naɗa sabon shugaban.
Haka kuma sanarwar ta ruwaito cewa, gwamnatin ta umurci tsohon Shugaban Ma’aikatan kan ya mika ragamar ofishin ga mai rikon mukamin a ranar Laraba 11 ga wantan nan da muke ciki na Maris.













































