Tinubu ya nemi sahalewar majalisar Dattawa kan tura sojoji zuwa Jamhuriyar Benin

Bola Tinubu Tinubu uk 750x430 (2)

Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya rubuta wa Majalisar Dattawa yana neman amincewar ta kan tura sojojin Najeriya zuwa Jamhuriyar Benin domin gudanar da ayyukan yaƙi a ƙasar maƙwabciya.

Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya karanta wasiƙar a zaman majalisa na ranar Talata, inda shugaban ƙasa ya bayyana gaggawar bukatar tura dakarun Najeriya.

Wasiƙar ta nuna cewa an aika da buƙatar ne bisa tanadin sashe na 5(5) na kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 da aka yi wa kwaskwarima, tare da la’akari da mahimmancin aikin kiyaye zaman lafiya a ƙasar ’yar uwa.

Shugaban ya bayyana cewa bukatar ta samo asali ne daga roƙon Jamhuriyar Benin na neman taimakon Najeriya wajen tabbatar da tsaro, musamman ganin kyakkyawar alaƙa ta zumunci da ɗan’uwan kai da ke tsakanin ƙasashen.

Karanta: Lalata yunƙurin juyin Mulkin Benin: Barau ya yaba da rawar da Tinubu ya taka, ya ce dimokuradiyya ita ce mafi dacewa

Sojoji ƙarƙashin Laftanar Kanar Pascal Tigri ke jagorantar tawagar sun mamaye gidan talabijin na ƙasar a Cotonou a ranar Lahadi tare da sanar da hambarar da gwamnatin Shugaba Patrice Talon, amma an dakile yunkurin ta hanyar jiragen yaƙi da dakarun da Najeriya ta tura.

Rahotanni sun ce matakin da Najeriya ta ɗauka na tura sojoji ya kasance wani ɓangare na ƙoƙarin tabbatar da zaman lafiya da daidaiton yankin, musamman bayan tashin hankali da ya kunno kai a ƙasar maƙwabciya.

Hukumomi sun bayyana cewa ƙarin bayani kan matakan da ake ɗauka zai fito nan gaba yayin da ake ci gaba da bibiyar halin da ake ciki a Jamhuriyar Benin.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here