Gwamnan Kano ya baiwa rundunar tsaro ta JTF tallafin Motoci da Babura

WhatsApp Image 2025 11 20 at 18.31.57 750x430

Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya karfafa aikin rundunar tsaro ta JTF a jihar ta hanyar bai wa jami’anta motoci Goma da Babura Hamsin domin inganta tsaro a yankuna da dama.

Tallafin ya dace da bukatar ƙara hanzarta kai ɗauki ga jami’an tsaro, musamman a kananan hukumomin Kiru, Tsanyawa, Kunchi, Ghari, Shanono, Tudun Wada da Doguwa da ke fama da matsalolin tsaro a lokuta daban-daban.

Gwamnatin jihar ta bayyana cewa an gudanar da bikin mika kayan aikin ne a Gidan gwamnatin Kano, karkashin jagorancin mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa.

Daraktan ayyuka na musamman, Umar Baba Zubairu, ya wakilci darakta-janar na sashen, Manjo Janar Sani Muhammad mai ritaya, wajen mika takardar amincewa da kayan aikin ga rundunar.

Shugaban rundunar JTF A.M Tukur ya samu wakilci ta hannun babban jami’in ofishinsa, tare da halartar wakilan kwamishinan ’yan sanda, daraktan DSS, kwamandan NSCDC da shugabannin kananan hukumomin Kiru, Tsanyawa da Gwarzo.

Gwamna Yusuf ya jaddada kudirin gwamnatinsa na ci gaba da fifita tsaro da tallafawa dukkan shirye-shiryen hadin gwiwa domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma a fadin jihar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here