Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Neja, NSEMA, ta ce ta gano gawarwaki 24 tare da ceto sama da mutane 30 a wani hatsarin kwale-kwale da ya afku a ranar Lahadi a karamar hukumar Mokwa ta jihar.
Mukaddashin Darakta Janar na Hukumar NSEMA, Alhaji Garba Salihu ne ya bayyana haka a ranar Lahadin da ta gabata yayin wata tattaunawa da kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) a Minna.
“NSEMA ta samu rahoton wani hatsarin kwale-kwale da ya afku tsakanin karfe 7:30 na safe zuwa karfe 8 na safiyar yau a tsakanin Jebba da Dam din Kainji a yankin Gbajibo a karamar hukumar Mokwa.
“Hukumar tare da hadin guiwar karamar hukumar Mokwa da masu ruwa da tsaki na al’umma suna gudanar da aikin bincike, ceto da kuma ceto a wurin da lamarin ya faru.










































