Majalisar Wakilai ta nemi hukumar dake kula da jami’o’i ta kasa NUC, data dakatar da yunkurin karin kudin makaranta a jami’o’in kasar nan.
Dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Dala a jihar Kano, Aliyu Sani Madaki ne ya kai kudin gaban majalisar a yau Talata.
Jaridar Solacebase ta rawaito cewa dan majalisar ya bayyana wasu daga cikin jami’o’in kasar nan da suka kara kudin makarantar su, wadan da suka hada da Jami’ar Bayero dake Kano, jami’ar Nsukka, University of Oyo, jami’ar Maiduguri, Michael Okpara University, jami’ar Dutse da sauran su.
Dan majalisar ya bayyana karin kudin makarantar a wani abu wanda zai sa ya yan talakawa su ajiye karatun su, saboda bazasu iya biyan kudin ba.
Dan majalisar ya kuma kara yin kira ga gwamnatin tarayya data sake duba kara kudin makarantun sakandare mallakin gwamnatin tarayya data yi.










































