Zargin ta’addanci: Kotu ta sake ƙin amincewa da bada belin Tukur Mamu karo na uku

Tukur Mamu 1 1 750x430

Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta sake ƙin amincewa da buƙatar bada belim da mai tattaunawa da ‘yan ta’adda, Tukur Mamu, wanda ya nema yayin da yake tsare a hannun hukumar tsaro ta farin kaya (DSS).

Mai shari’a Mohammed Umar ya yanke hukuncin cewa hukumar DSS ta kai Mamu asibiti domin samun kulawar likita bayan da aka kawo korafin rashin lafiyarsa.

Kotun ta bayyana cewa ɗaya daga cikin dalilai bayar na ba da beli shi ne rashin jajircewar masu shigar da ƙara, amma a wannan lokaci gwamnati ta nuna jajircewa wajen bin shari’ar, don haka ba za a bayar da belin ba.

Mai shari’ar ya kuma ce Mamu bai kawo hujjoji masu ƙarfi da za su sa kotu ta amince da bukatar sa ta beli ba, domin bayar da beli lamari ne da ake yi da kulawa da hujja mai inganci.

Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya bayyana cewa wannan shi ne karo na uku da kotun ta ƙi amincewa da buƙatar belin Mamu tun bayan gurfanar da shi a ranar 21 ga Maris, 2023 bisa zargin tallafawa ayyukan ta’addanci.

An kama Mamu a filin jirgin saman ƙasa da ƙasa na Cairo a ranar 7 ga Satumba, 2022 bisa zargin haɗin gwiwa da ‘yan ta’addar Boko Haram wajen karɓar kuɗin fansa daga iyalan fasinjojin jirgin ƙasa da aka sace daga Abuja zuwa Kaduna.

Kotun ta ci gaba da sauraron shari’ar Mamu a gaban mai shari’a Umar, inda ya ci gaba da musanta laifin da ake zarginsa da shi.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here